Hatsarin Kwale-Kwale ya yi Sanadiyar Mutuwar Mutane Hudu a Borno

 

Borno – Rahotanni sun bayyana cewa wani hatsarin kwale-kwale yayi sanadiyar mutuwar mutane hudu a garin Dikwa da ke jihar Borno.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Borno, ASP Nahum Daso ya sanar da cewa sun samu rahoton iftila’in ne a hedikwatar ‘yan sandan Dikwa.

Kwale kwale ya yi hatsari a Borno

Tashar Channels TV ta ruwaito ASP Nahum Daso ya ce rundunar ta samu rahoton cewa wani mummunan hatsarin kwale-kwale ya afku a ranar Litinin.

Jami’in rundunar ya ce hatsarin jirgin ruwan ya faru a yankin Bakassi, tsakanin Mafa da Dikwa kan hanyar Maiduguri, jihar Borno.

Sanarwar ‘yan sandan ta ce hatsarin ya rutsa da kwale-kwalen da ke dauke da fasinjoji inda ya nutse a cikin ruwa, wanda hakan ya yi sanadin rasa rayukan mata hudu.

Hatsarin ya yi sanadiyar mutuwar matan hudu da suka fito daga unguwar Bulabulin da ke Dikwa.

Mata 4 sun mutu a hatsarin Borno

Wadanda suka mutu a hatsarin sun hada da Ya Mallum Shettima, wata babbar mace ‘yar karamar hukumar Marte da Maimuna Akura ‘yar shekara 10.

Sauran matan su ne: Umira Alhaji Bulama ‘yar shekara 6, sai kuma Yagana Bulama Kawu mai wata biyar da haihuwa.

Ba tare da bata lokaci ba aka kwashe matan zuwa babban asibitin Dikwa, inda likitoci suka tabbatar da rasuwarsu inji rahoton jaridar Vanguad.

Bayan haka, an mika gawarwakin ga iyalansu domin yi musu jana’iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here