Kano: Yadda Wani Hatsarin Mota ya yi Sanadiyar Rasa Rayuka

 

Har ila yau, ana asaran rayuka a titunan Najeriya sakamakon hadarin mota.

Rashin kyawun hanya, karancin ma’aikata da kayan aiki babban tsaiko ne ga jami’an hukumar FRSC.

Direbobi na da nasu laifin na kure gudu a manyan hanyoyi Mummunan hadarin motan da ya faru a Kwanar Garko dake karamar hukumar Garko ta jihar Kano, ya yi sanadiyar halakar akalla mutane 11, Daily Trust ta ruwaito.

Hadarin wanda ya faru daidai kauyen Dakare a hanyar Garko misalin karfe 10 na safiyar Alhamis tsakanin motoci biyu kirar Toyota Hiace da Volkswagen Sharon.

Mutane takwas sun mutu nan take yayinda wasu uku suka cika a asibiti bayan an kaisu jinya.

An tattaro cewa yawancin matafiyan yan kasuwa ne da suke hanyar zuwa kasuwar Darki dake karamar hukumar Wudil.

Tabbatar da labarin, kakakin hukumar kiyaye hanyoyi da hadura FRSC na jihar, Kabiru Daura, ya ce mutane 20 hadarin ya shafa kuma 6 na kwance yanzu a asibiti.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here