Kungiyar HEDA ta Gano Kadarorin Tsofaffin Manyan ‘Yan Siyasan Najariya da Suka Mallaka a Dubai

 

Wata kungiyar yaki da cin hanci da rashawa ta bankado wata babbar badakala.

Ta bayyana cewa, ta gano wasu kadarori da wasu tsofaffin gwamnoni suka mallaka.

Ta kuma bada rahoton da ta hada ga shugaban EFCC don gudanar da bincike Kungiyar yaki da cin hanci da rashawa ta Human and Development Debelopment Agenda, (HEDA) ta bankado wasu kadarori da wasu fitattun ‘yan siyasan Najeriya suka mallaka a Dubai, Hadaddiyar Daular Larabawa.

Rahoton, wanda kungiyar HEDA ta hada ita ce ta dauki nauyin shi, amma Farfesa Gbenga Oduntan na jami’ar Kent ne ya yi bincike tare da hada shi.

Ya bayyana cewa, wasu tsofoffin gwamoni, ministoci da sanatoci sun mallaki wasu manyan kadarori 130 a Dubai da ake zargin sun mallakesu ne ta hanyar wawashe dukiya daga Najeriya.

Kadarorin suna daga cikin sama da 800 da aka gano mallakar ‘yan Najeriya a cikin Hadaddiyar Daular Larabawa da suka hada da manyan hafsoshin tsaro da sojoji.

Sun kuma samu ne daga cin hanci da rashawa, kauracewa haraji na kasuwanci, haramtattun ayyuka da kungiyoyi da kamfanonin kasuwanci ke yi da kuma sakamakon da aka samu daga ayyukan laifi.

Ko da yake rahoton bai bayyana ainihin ‘yan siyasan da suka mallaki kadarorin a Dubai ba, Shugaban HEDA, Olanrewaju Suraj, wanda ya yi magana da jaridar The Nation ta wayar tarho a daren jiya, ya ce: “Mun bar wa EFCC don warware badakalar.

Abin takaici ne matuka cewa ana wawure kudadenmu ana boye su a kasashen waje.

“Ba ma kawai maganar kadarori a cikin Hadaddiyar Daular Larabawa da aka gano mallakar wasu hafsoshin soja ba.”

Yayin karbar rahoton, shugaban hukumar ta EFCC, Bawa, ya ce: “Ina so na tabbatar muku cewa za mu yi nazarin rahoton domin mu kara darajar wadancan wuraren da yake cikin aikin mu; za mu dube shi kuma mu tabbatar da cewa an yi adalci.

“An dade ana cutar kasar nan, mutanen da aka dora masu nauyin gudanar da mulki a kasar nan sun yi nasarar yin hakan saboda son kai ta hanyar wawashe wadannan kudade daga kasar nan zuwa waje.

Ya ba da tabbacin dakatar da irin wannan badakalar anan gaba tare da tabbatar da dawo da dukiyoyin kasa Najeriya.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here