Fatakwal Zuwa Bonny: Mutane Sun Mutu Sanadiyyar Bude Wuta da Helikafta ya yi wa Jirgin Ruwa

 

Wani jirgi mai saukan ungulu da ba a tabbatar na wanene ba ya bude wa jirgin ruwa wuta a Bonny.

Wani ganau ya bayyana cewa jirgin ruwan ya tashi daga Bonny ne yana kan hanyarsa na zuwa Fatakwal.

Shaidan ganin na ido ya bayyana cewa wasu daga cikin mutanen jirgin sun mutu yayin da saura an garzaya da su asibiti.

Jahar Rivers – Wani jirgi mai saukan ungulu da a yanzu ba a gano mallakar waye ba ya harbi wani jirgin ruwa mai dauke da fasinjoji daga Fatakwal zuwa Bonny a jahar Rivers, The Punch ta rawaito.

Ana fargabar wasu sun mutu, yayin da wasu daga cikin wadanda ke cikin jirgin an kwashe su zuwa asibiti.

Abin da wani ganau ya ce game da afkuwar lamarin?

Wani shaidan gani da ido a bakin ruwa na Bonny-Nembe inda abin ya faru ya ce jirgin ya taso ne daga Fatakwal, ya kuma shaidawa manema labarai akwai wadanda suka mutu, a cewar SaharaReporters.

Yayin da ya ke bayyana fargabarsa kan faruwar lamarin, ya ce jirgin ruwan na dauke da fasinjoji da kayan abinci.

Ya yi ikirarin cewa:

“Jirgin ruwan bai dade da barin nan Bonny ba, a tsibirin, wata helicofta ko jirgi mai saukan ungulu, kawai ta zo ta baya, ta sako kasa-kasa ta fara budewa jirgin ruwan na katako wuta.

“Daga bayannan da muka samu daga direban jirgin ruwan, akwai fasinjoji a jirgin, Kazalika akawai kayan abinci kamar garin rogo, shinkafa da wasu kayan abincin.

“Kowa ya san cewa wannan ne hanyar da ake jigilar abinci zuwa Bonny. Wasu mutane sun mutu a cikin jirgin ruwan.”

Ba a samu ji ta bakin hukumomin tsaro ba

Da aka tuntube shi, kakakin yan sandan jahar Rivers, Nnamdi Omoni ya ce bai riga ya samu rahoton ba.

Kakakin sojojin Nigeria, 6 Division, Charles Ekeocha, shi kuma bai daga wayarsa ba, haka ma takwararsa na rundunar sojojin sama a Fatawal, a lokacin hada wannan rahoton.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here