Hisbah Tayi Nasarar Kama ‘Dan Sandan da yake Bata Tarbiyyar Yara Mata

 

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama wani Basiru a wani gida yana lalata da wata yarinya mai karancin shekaru.

Mahaifin yarinyar ya ce ya nemi yarinyar sama ko kasa bai ganta ba na tsawon kwana 2, ashe tana wurin Basiru.

Hukumar ta na neman har da abokinsa, Jamilu, wanda ya gina gida musamman don yin lalata da mata.

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama wani dan sanda Basiru a wuraren Rumawa da ke karamar hukumar Ungogo a kan laifin lalata, Vanguard ta wallafa.

Kamar yadda hukumar tace, an kama har da Basiru abokin Jamilu a wani daki da ke wuraren Rumawa, inda suka boye suna aikata alfashar.

Mazauna Rumawa sun yi gaggawar sanar da yadda Basiru da abokin sharholiyarsa suka makale a wani daki suna lalata da wata yarinya mai karancin shekaru, wacce iyayenta suka yi ta neman ta amma basu ganta ba.

Marikin yarinyar, Usman Ahmad ya ce ya yi ta neman diyarsa bai ganta ba, sai daga baya ya gano tana hannun hukuma.

“Basiru, abokin Jamilu ya gina gida a Rumawa musamman don yin lalata da kananan yara da sauransu.

“Na kan nemi yarinyata kwana biyu in rasa ta. Wannan karon na nemeta na kwana 2 ban ganta ba, ashe tana dakin wadannan mutanen,” cewar marikinta.

Ya kara da cewa, “an kama Basiru da Jamilu, mai gidan da ake lalatar. Sannan an mayar da al’amarin a hannun ‘yan sanda don su cigaba da bincike.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here