Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama Matasa 21

 

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta ce ta kama wasu matasa 21 a wani otel da ke yankin Kureken Sani a ƙaramar hukumar Kumbotso bisa zargin aikata abubuwan da suka saɓa wa dokokin addini.

Mataimakin Babban Kwamandan hukumar, Dakta Mujahid Aminuddeen, ya tabbatar wa jaridar Daily Trust faruwar lamarin, inda ya ce an kama mata 11, wasu daga cikinsu na da shekaru tsakanin 17 zuwa 25.

Ya ƙara da cewa an kama maza 10, mafi yawansu matasa da shekarunsu ba su wuce 30 ba.

A cewarsa, an cafke mutanen ne yayin da ake zargin suna shirya wani taro da ya saɓa wa dokokin Hisbah.

Aminuddeen ya kuma bayyana cewa an kama manajan otel din dangane da wannan lamari.

Ya ce za a gurfanar da waɗanda aka kama a gaban kotu domin fuskantar hukunci daidai da doka.

Haka kuma, ya buƙaci al’umma da su riƙa sanya ido tare da kai rahoton duk wani abu da suke zargi, musamman wanda ya shafi kananan yara, ga hukumomin da suka dace.

Wannan kamen na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan da hukumar ta sanar da kama matasa sama da 600 bisa zargin aikata abubuwan da ba su dace ba a lokacin bukukuwan Sallah da suka gabata.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here