Zahra Bayero: Hukumar Hisbah ta Jahar Kano ta yi Magana Kan Shigar Amaryar Yusuf Buhari
Bayan kwanaki da bikin Bridal Shower, Hisbah ta mayar da martani ga jama’a.
Kwamandan Hizbah ya ce laifi ne a addini cigaba da yada hotunan a kafofin sada zumunta.
Manyan malamai sun ce wannan abu da diyar Sarkin tayi bai dace ba.
Kano – Hukumar Hisbah masu tabbatar da dabbaka koyarwan addinin Musulunci a jahar Kano ta yi magana daga karshe kan hotunan da sukayi yawo na diyar Sarkin Bichi, Zahra Nasir Bayero.
Read Also:
Zahra Nasir Bayero, budurwa ce ga ‘dan gidan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Yusuf Buhari, kuma ana shirin daura musu aure.
Zahra Bayero da kawayenta sun gudanar da bikin share faggen daurin aure ‘Bridal Shower’ kuma hotunan shagalin sun tayar da kura.
Jama’an Najeriya sun zargi hukumar Hisbah da son kai saboda ta ki magana kan lamarin don ‘yayan masu fada a ji ne, sabanin abinda ake yiwa ‘yayan talakawa a Kano idan sukayi irin haka.
Amma kwamandan Hisbah, Sheikh Harun Ibn Sina ya bayyanawa BBC cewa diyar Sarkin bata fi karfin doka ba kuma ya kamata ace ta nuna ita yar gidan manya ne idan tana neman albarka a aurenta.
Hakazalika Ibn Sina ya caccaki mutanen da ke yada hotunan da bidiyoyin Zahra Bayero inda yace laifi ne yada ire-iren hotunan.