Ziyara: Hotunan Shugaba Buhari a Jahar Imo
A ranar Alhamis ne shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ziyarci jahar Imo da ke kudu maso gabashin kasar.
Shugaban ya samu gagarumar tarba daga ‘yan jahar, duk da kiran da kungiyar ‘yan a-aware ta IPOB ta yi kan mutane su zauna a gidajensu.
Buhari ya kaddamar da jerin ayyukan da gwamnatinsa da ma gwamnatin jahar suka yi a jahar.
Ga wasu hotunan ziyarar shugaban kasar:
A cikin ayyukan da Shugaba Buhari ya kaddamar har da tashar karkashin kasa mai suna Chukwuka Nwoha.
Haka kuma ya kaddamar da hanyar Naze zuwa Nekede zuwa Ihiagwa.
Kazalika ya kaddamar da titin Egbeada da ke Amakohia
Shugaba Buhari ya kuma bude sabon dakin taron majalisar zartarwar jahar da ke Gidan Gwamnatin jahar mai suna Douglas House
Shugaba Buhari ya gana da wasu shugabannin Kudu maso Gabas.
Read Also:
Ziyarar tasa tana da muhimmanci ganin cewa gwamnan jahar Imo Hope Uzodimma, wanda dan jam’iyyar APC ne, yana daga cikin shugabannin yankin da ke goyon bayan manufofin shugaban kasar.
Shugaba Buhari ya gana da wasu shugabannin Kudu maso Gabas
Masu fada a ji na yankin mun jinjina wa Buhari kan ayyukan da yake yi na ci gaban kasa
Da ma dai gwamnonin yankin sun yi kira ga mazauna jahar su fito kwansu da kwarkwatarsu domin tarbar shugaban kasar
Sai dai an rufe wasu kasuwannin da ke kusa da wuraren da shugaban ya kai ziyara domin tabbatar da tsaro
Wannan yankin na Orlu na cikin wuaren da Shugaba Buhari ya kaddamar da ayyuka
Tsohuwar kasuwar Orlu babu kowa a yayin da Buhari ya ziyarci jahar Imo
sha tale-talen Orlu bayan shugaban kasa ya ziyarci jahar Imo