Hotunan Ziyarar da Sheikh Dahiru Bauchi ya Kai Fadar Shugaban Kasa

 

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da Sheikh Dahiru Bauchi a fadar shugaban kasa.

Sheikh Dahiru Bauchi ya samu rakiyar ministan sadarwa, Sheikh Dr Isa Ali Ibrahim Pantami.

Legit Hausa ta samo hotunan ganawar tasu, sannan ta kawo muku rahoton ganawar tasu.

Abuja – Shugaban kasa, Manjo Janar Muhammdu Buhari (mai ritaya), ya karbi bakuncin jagoran darikar Tijjaniyya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi a fadar gwamnati da ke Abuja ranar Alhamis 19 ga watan Agusta, 2021.

Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Femi Adesina ne ya watsa hotunan ganawar tasu a kafar Facebook.

Ya rubuta cewa:

“Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Shahararren Malamin Addinin Musulunci kuma Jagoran Darikar Tijjaniyya Sheikh Dahiru Usman Bauchi a gidan gwamnati a ranar 19 ga Aug 2021.”

Sheikh ya samu rakiyar Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Dijital, Sheikh Dr Isa Pantami.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here