Hukumar EFCC ta Gurfanar da A.A Zaura Kan Zambar Dala Miliyan 1.320
Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin Najeriya zagon ƙasa ta gurfanar da ɗan takarar Majalisar Dattawa na Kano ta Tsakiya na jam’iyyar APC, AA Zaura a kotu.
EFCC ta gurfanar da ɗan takarar ne wanda cikakken sunansa shi ne Abdulsalam Abdulkarim Zaura a gaban wata babbar kotun tarayya a Kano a yau Laraba 1 ga watan Maris, 2023 a bisa zargin laifuka huɗu da suka danganci zamba.
Read Also:
A ɗaya daga cikin laifukan da aka karanta masa a kotun wadda mai shari’a Mohammed Nasir Yunusa ya jagoranta, an zarge shi da cewa a wani lokaci a watan Agusta na 2014, ya karɓi dala dubu 200 daga Dr Jamman Al- Azmi a kano, da nufin zamba, da karyar za su yi wata harkar kasuwanci ta haɗin gwiwa
Wanda ake zargin ya musanta aikata laifin da ake tuhumarsa da shi, bayan lauya mai gabatar da ƙara Aisha Tahar Habib ta karanta masa.
Lauyan AA Zauran, Ishaq Mudi Dikko,( SAN) ya nemi kotu ta bayar da belin wanda yake karewa, inda bayan ‘yar taƙaddama, alkalin kotun, Justice Yunusa ya amince da belin.
Yanzu dai an ɗage shari’ar har zuwa ranar 2 ga watan Mayu na 2023 domin fara saurare.
Za a fara shari’ar ne tun daga farko bayan da kotun ɗaukaka ƙara ta soke saki da kuma wanke wanda ake zargin a kan laifin zamba da alkalin babbar kotun tarayya a Kano A. L. Allagoa ya yi a baya.
Ana zargin A.A Zaura da zambatar wani ɗan ƙasar Kuwait dala miliyan 1,320,000, a kan cewa shi ɗan kasuwa ne da ke harkar gidaje a Dubai da Kuwait da kuma wasu ƙasashen Larabawa