Hukuncin da Kotun Jahar Kano ta Yanke wa Mutumin da ya Kashe Matarsa 
Wata kotu ta yanke wa wani mutumi hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa kama shi da laifin hallaka matarsa.
 Mutumin mai suna, Aminu Inuwa, ya musanta abinda ake zarginsa da shi, a cewarsa sam ba shine ya kashe matarsa ba.
 Amma masu gabatar da ƙara sun tabbatar da cewa shi ya aikata ƙisan bayan wani sa-insa ya haɗa shi da matar a ɗakin girki.
Kano – Wata babbar kotu a jahar Kano, ranar Talata, ta yankewa wani mutumi, Aminu Inuwa hukuncin kisa ta hanyar rataya.
 Daily Nigerian ta rahoto cewa kotu da kama mutumin da laifin kashe matarsa, Safara’u Mamman.
Malam Inuwa, wanda bamu gano haƙiƙanin shekarunsa ba, yana zaune ne a Gwazaye Quarters dake Ɗorayi babba, cikin jahar Kano.
Alkalin kotun, Mai shari’a Usman Na’abba, ya bayyana cewa hujjoji sun tabbatar da laifin wanda ake ƙara ba tare da tantama ba.
Yaushe mutumin ya kashe matarsa?
 Kafin yanke hukuncin, mai gabatar da ƙara Lamido Sorondinki, ya shaidawa kotu cewa mutumin ya aikata laifin ne a ranar 2 ga watan Afrilu, 2019.
 Sorondinki ya kara da cewa:
 “Wanda ake zargin ya jiwa matarsa rauni a maƙogwaro da wukar daƙin girki lokacin da wata gardama ta haɗa su.”
“Bayan ya tabbatar da ta mutu, sai ya haƙa mata kabari ya binne ta a wani karamin ɗaki da ba’a ƙarisa ba dake gidansa a Ɗorayi Babba.”
Mai gabatar da ƙarar ya gabatar da shaidu 3 da kuma mutum 6 da aka nuna wa domin tabbatar da laifin wanda ake zargi.
Shin mutumin ya amsa laifinsa?
A ɗaya ɓangaren kuwa, wanda aƙe ƙarar, Malam Inuwa, ya musanta maganar mai gabatar da ƙara, inda yace ba shine ya kashe matarsa ba.
Lauyan dake kare wanda ake ƙara, Mustapha Idris, ya gabatar da shaidu uku domin kare Malam Inuwa.
 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here