Sheikh Dahiru Bauchi ya Nemi Gwamnati ta Hukunta Wadanda Suke da Hannu a Kisan Matafiya a Jos

 

Dahiru Usman Bauchi yana so a hukunta wadanda suka kashe Bayin Allah a jahar Filato.

Shehin malamin ya bukaci a biya iyalan wadanda suka rasu diyya, a kula da masu rauni.

Malamin yace an dade ana wannan, yana so ayi alkawari hakan ba zai sake aukuwa ba.

Bauchi – Babban malamin addinin musulunci, Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya bukaci gwamnati ta hukunta wadanda ke da hannu wajen kashe matafiya a Jos.

BBC Hausa ta yi hira da shehin malamin, inda ya bayyana cewa an kure masu hakuri wannan karo, ganin yadda aka dade ana kashe masu mutane a Najeriya.

“InnaliLahi wa inna ilaihi rajiun!” “InnaliLahi wa inna ilaihi rajiun! “InnaliLahi wa inna ilaihi rajiun!! “InnaliLahi wa inna ilaihi rajiun!!! “Mu wannan abu, an dade ana yi mana, ‘yanuwa da suke zuwa zikiri ake tsare wa, ana kashe wa. Ba za mu yafe ba, ba za mu bari ba, ba za mu yi shiru ba.”

“Za mu dauki dukkan matakai da za a dauka wadanda shari’a ta yadda da su. Mu na kiran musulmai, muna bada hakuri cewa ka da a dauki mataki a hannu.”

“Ayi hakuri, muna bin gwamnati har mu ga inda suka tsaya. Idan inda suka tsaya bai yi mana ba, sai mu yi namu.”

Wani mataki Shehi yake so a dauka?

Shehin yace na farko a biya diyyar wadanda aka kashe ga iyalansu, na biyu a hukunta wadanda suka yi laifin, kuma a dauki dawainiyar wadanda aka ji wa rauni.

“Sannan a dauki alkawari irin wannan abu ya zo karshe kenan, an katse shi ba zai kara faru wa ba.”

Malamin ya fadawa BBC idan masu rike da mukamai ba za su iya kare rayuka da dukiyoyin al’umma ba, su sauka daga kujerunsu, su bari wasu su karbi mulkin.

“Amma hakika an kure mu, an kure mana bakin hakurinmu. Mun fada a lalama, mun fada a cikin zafi.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here