Jahohin Najeriya 5 da Suka Bada Hutun Sabuwar Shekarar Musulunci
Ranar farkon sabuwar shekarar Hijra zai kama ranar Litinin ko Talata dangane da ranar da aka ga wata. Don murnar wannan shekara ta 1443 bayan Hijra, wasu jahohin Najeriya sun bada hutu ga al’ummarsu.
Legit ta hararo muku jahohi biyar da za’a yi hutu don murnar ranar:
1. Jahar Osun
Gwamnan jahar Osun, Gboyega Oyetola, ya sanar da ranar Litinin, 9 ga Agusta, a matsayin ranar hutu don murnar shiga sabuwar shekarar
Musulunci – Hijrah 1443 AH. Wannan na kunshe cikin jawabin da Kwamishanan harkokin cikin gidan jahar, Tajudeen Lawal, ranar Juma’a a Osogbo, rahoton NAN.
2. Jahar Oyo
Gwamnatun jahar Oyo, ta sanar da ranar Talata, 10 ga watan Agusta, a matsayin ranar hutu don murnar shiga sabuwar shekarar Musulunci – Hijrah 1443 AH.
Read Also:
Wannan na kunshe cikin jawabin da Sakataren gwamnatin jahar, Mrs Olubamiwo Adeosun, ta saki ranar Juma’a a Ibadan, babbar birnin jahar, rahoton Tribune.
Gwamnan ya yi kira ga Musulmai da masu bin sauran addinai suyi amfani da hutun domin addu’a ga cigaban jahar da Najeriya gaba daya.
3. Jahar Kano
Gwamnan jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya alanta ranar Litinin, 9 ga Agusta, a matsayin ranar hutu don murnar shiga sabuwar shekarar Musulunci – Hijrah 1443.
Wannan na kunshe cikin jawabin da kwamishanan labaran, Muhammad Garba, ya saki ranar Juma’a.
4. Jahar Jigawa
Gwamnatin jahar Jigawa ta sanar da ranar Litinin, 9 ga Agusta, a matsayin ranar hutu don murnar shiga sabuwar shekarar Musulunci.
Ya yi kira da mutan jahar suyi amfani da wannan dama wajen yiwa jahar addu’a kan halin rashin tsaron ake ciki.
5. Jahar Kebbi
Gwamnan jahar Kebbi, Abubakar Atiku Bagudu ya bi sahun takwararorin na bada hutun sabuwar shekarar Musulunci.
Wannan na kunshe cikin jawabin da aka saki a birnin Kebbi.