Mafi Yawancin Jami’an ‘Yan Sanda ba Kasa Suke Tsarewa ba – Tsohon IGP
Tsohon Sifeton yan sanda, Solomon Arase, ya fasa kwai.
Ya ce yan sandan Najeriya masu kudi kadai suke tsaro, maimakon daukacin yan Najeriya Tsohon Sifeto Janar na yan sanda, Solomon Arase, ya ce sama da yan sanda 200,000 ake baiwa manyan yan siyasa maimakon tsaron al’ummar Najeriya milyan 200.
Ya bayyana hakana a jawabin da yayi a tattaunawar makarantar koyar da ilmin shugabanci na tsohon gwamnan jihar Ogun, Otunba Gbenga Daniel, dake Abekuta, Daily Trust ta ruwaito.
“Muna da yan sanda 400,000 a Najeriya, amma 200,000 na tare da yan siyasa.
Abinda muke a kasar nan kawai yan siyasa ake tsaro, ba ma tsaron jama’a, kuma abinda ya kamata mu duba ne,” Arase yace.
Arase ya ce ummul haba’isin matsalolin da ake samu a hukumar yan sandan Najeriya rashin son gyaran yan siyasa ne.
Read Also:
Yace tun shekarar 1999, Najeriya ta yi kwamitocin gygyara hukumar har guda hudu “amma kaico, babu gyaran da akayi amfani a shi.Takardun na nan an ajiyesu suna rufe da kura.”
Wannan ya biyo bayan umurnin da Sifeton yan sanda ya baiwa manyan jami’ansa a karshen makon da ya gabata. Sifeto Janar na yan sanda, Mohammed Adamu, ya bada umurnin janye dogaran dake wajen attajirin dan kasuwa, Emeka Offor; Fani-Kayode, manyan malamai da kamfanoni da fadin tarayya.
Wannan umurni ya shafi mutane 60, kamfanoni, cocuna da kungiyoyin addini.
Daga ciki akwai Christ Embassy, Think Nigeria First Initiative, Uche Sylva International, Stanel Groups, da KYC Holding Sauran sune Sen Lado Yakubu, Amb. Yuguda Bashir, Uche Chukwu, Sen.
Boroface Ajayi, Mutiu Nicholas, Sen. Tokunbo Afikuyomi, Edozie Madu, David Adesanya, Chris Giwa, Chief Godwin Ekpo, Chief Pius Akinyelure da sauransu.
Hakan na kunshe cikin wasika mai lamba .CB: 4001/IGP.SEC/ABJ/VOL.116/32 da rana wata 4 ga Nuwamba, da IGP ya aikewa dukkan kwamishanonin yan sandan jihohin Najeriya 36 da birnin tarayya.