INEC ta Canza wa Shugabanninta na Jahohi Guda 5 Daga Inda Suke Aiki Zuwa Wata Jahar

 

Hukumar zaɓe ta ƙasa INEC ta yi wasu muhimman canje-canje a wasu jahohin ƙasar nan.

INEC ta tura wasu shugabanninta na jahohi (REC) zuwa wasu jahohi na daban yayin da aka maye gurbinsu da wasu.

Shugaban kwamitin yaɗa labarai, Festus Okoye, shine ya sanar da haka a Abuja ranar Lahadi.

Abuja – Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta sanar da yin garambawul na canza wasu shugabanninta na jahohi, kamar yadda dailytrust ta rawaito.

Hukumar ta canza wa wasu shugabanninta na jahohi (RECs) guda biyar daga inda suke aiki zuwa wata jahar, kamar yadda the cable ta rawaito.

Festus Okoye, kwamishinan hukumar na ƙasa kuma shugaban kwamitin yaɗa labarai, shine ya sanar da haka ranar Lahadi a Abuja, ya kara cewa canjin ya shafi wasu daraktoci huɗu.

A cewar Okoye, sabon jadawalin aikin ya maida REC na jahar Osun, Mr. Olusegun Agbaje, zuwa jahar Ogun, yayin da takwaransa na jahar Ogun, Farfesa AbdulGaniy Olayinka Raji, zai maye gurbinsa a Osun.

A jawabinsa yace:

“REC na jahar Bayelsa, Dr. Cyril Omorogbe, zai koma jahar Cross Rivers yayin da na jahar, Emannuel Alex Hart zai maye gurbinsa a Jahar Bayelsa.”

“Hakanan an maida shugaban INEC na jahar Zamfara, Dr. Asmau Sani Maikuɗi, zuwa jahar Kaduna.”

INEC ta yi gyara a wasu daraktoci

Hukumar ta kuma bayyana cewa daraktan wayar da kan masu kaɗa kuri’a, Mr. Nick Dazang, ya tafi hutun zango bisa haka Mr. Victor Ayodele zai maye gurbinsa.

Hakanan kuma INEC ta sanar da maida, Mista Mikah Thabbal Lakumna zuwa matsayin daraktan sashin shugabanci, daga matsayinsa na daraktan tsaro.

Hukumar tace, Mista Nduh Lebari Samson, zai koma matsayin daraktan tsaro daga ofishin sakataren INEC, yayin da daraktan sashin ayyukan zaɓe, Yakubu Muhammed Duku, zai koma jahar Neja a matsayin sakatare.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here