Hukumar INEC ta Sanar da Ranar Karshe da za ta Fitar da Sunayen Dukkan ‘Yan Takara a Zaben 2023

 

Hukumar shirya zabe ta INEC za ta fitar da sunayen wadanda za’a gani ranar zabe a 2023 .

Hukumar INEC za ta gudanar zaben shugaban kasa ranar 28 ga watan Febrairu 2023 sannan na gwamna bayan makonni 2.

Shugaba Buhari ya yiwa yan Najeriya alkawarin cewa ba zai yi katsalandan a zaben 2023 ba.

Abuja – Hukumar gudanar da zabe ta kasa mai zaman kanta, INEC, za ta saki sunayen dukkan yan takaran da zasu yi musharaka a zaben kasa na shekarar 2023.

Shugaban hukumar, Farfesa Mahmoud Yakubu, ya bayyana hakan ne ranar Alhamis a Abuja inda ya halarci taron kungiyar Centre for Democracy and Development (CDD).

A cewarsa, hukumar zata saki sunayen yan takaran shugaban kasa, Sanatoci da yan majalisar wakilai ranar 20 ga Satumba, 2022, rahoton Channels.

Yayinda za’a saki na gwamnoni da majalisar jiha ranar 4 ga Oktoba.

Hakazalika ya bayyana ranar da za’a fara kamfe da kuma halin rashin tsaron da ake ciki a wasu sassan Najeriya, riwayar TheNation.

A cewarsa:ahm

“Harkokin zaben 2023 zasu yi zafi a watan nan.Nan da ranar 19 ga Satumba 2022, hukumar zata wallafa sunayen karshe na yan takaran shugaban kasa, Sanatoci da Majalisar wakilai, kamar yadda sashe 32(1) na dokar zabe ya tanada.”

“Bayan haka ranar 4 ga Oktoba za’a saki sunayen yan takaran kujerar gwamna da yan majalisar jiha.”

“Za’a fara kamfe ranar 28 ga Satumba, 2022. Idan aka fara, muna kira ga jam’iyyun siyasa da yan takara su mayar da hankali kan abubuwa masu muhimmanci.”

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here