PDP Zuwa APGA: Hukumar INEC ta Canza Sunan ɗan Takarar Gwamna a Jahar Anambra

 

Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta sake fitar da sunayen yan takarar gwamna a zaɓen Anambra dake tafe.

Har yanzun dai INEC bata sanya sunan ɗan takarar PDP ba a cikin waɗanda zasu fafata a zaɓen.

INEC ta bayyana cewa zata fitar da sunayen yan takara na karshe ranar 7 ga watan Oktoba.

Abuja – Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta canza sunan Michael Umeoji, zuwa Chukwuma Soludo, a matsayin ɗan takarar gwamnan Anambra karkashin jam’iyyar APGA.

Hakazalika, INEC ba ta sanya jam’iyyar PDP ba a jerin waɗanda ta tantance zasu fafata a zaɓen gwamnan dake tafe ranar 6 ga watan Nuwamba 2021, kamar yadda punch ta rawaito.

Kwamishinan INEC kuma shugaban kwamitin yaɗa labarai, Festus Okoye, shine ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis a Abuja.

Kwamishinan yace:

“INEC ta zauna yau 19 ga watan Agusta 2021, kuma an tattauna abubuwa da dama, wanda ya haɗa da tsayar da yan takara a zaɓen gwamnan Anambra dake tafe ranar 6 ga watan Nuwamba.”

“Jadawali da kuma tsarin ayyukan zaɓen da hukumar ta fitar ranar 18 ga watan Janairu, ya bada damar cirewa da maye ɗan takarar jam’iyya bisa dokar sashi na 35 ta kundin dokokin zaɓe.”

“INEC ta yi amfani da hukuncin kotun ɗaukaka kara ta Kano, wanda ya soke hukuncin babbar kotun Jigawa kan shugabancin jam’iyyar APGA da kuma ɗan takararta a zaɓen gwamnan Anambra.”

Yaushe INEC zata fitar da sunayen yan takara na karshe?

INEC Ta bayyana cewa a ranar 7 ga watan Octoba zata fitar sunayen yan takarar jam’iyyu na karshe, waɗanda zasu fafata a zaɓen gwamna ranar 6 ga watan Nuwamba.

Hukumar tace wannan duk yana cikin jadawalin yadda ayyukan zaɓen zai gudana wanda ta fitar tun a baya.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here