Zaɓen Gwamnoni: Kotu ta Yarda INEC ta Sake Saita Na’urar BVAS
Kotun ɗaukaka ƙara a Najeriya ta amince da buƙatar hukumar zaɓe ta ƙasar ta sake saita na’urar tantance masu zaɓe ta BVAS wadda aka yi amfani da ita a zaɓen shugaban ƙasa ranar 25 ga watan Fabirairu.
Tawagar alƙalan kotun mai mutum uku ƙarƙashin jagorancin Joseph Ikyegh ta yanke hukuncin cewa an bai wa INEC damar ne domin gudanar da zaɓen gwamnoni ranar Asabar 11 ga watan Maris.
Hukuncin na nufin kotun ta ƙi amincewa da buƙatar da ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar LP Peter Obi ya shigar ta neman hana INEC goge bayanan masu zaɓen da aka naɗa a zaɓen shugaban ƙasar.
Tawagar alƙalan ta ce INEC ta bayyana cewa tana da shirin kwashe bayannan da ke cikin na’urar 176,000 da aka yi amfani da su a zaɓen ta wallafa su a wani rumbun bayananta na daban, ko da yake Obi da LP ba su nuna ƙin amincewa da wannan shiri ba.
Tun da fari Mista Obi na jam’iyyar Labour ya shigar da ƙarar INEC a kotu kan zargin hukumar ba ta yi amfani da na’urar BVAS yadda ya dace ba, abin da ya sa suka gaza yin nasara a zaɓen, wanda aka bayyana Bola Tinubu na APC a matsayin wanda ya yi nasara.
Lauyan Obi, Onyechi Ikpeazu, yace dalilin shigar da ƙarar da suka yi shi ne don su cire bayanan da aka wallafa a cikin BVAS ɗin, na ainihin sakamakon da aka wallafa tun daga rumfunan zaɓen.
Ikpeazu ya ce idan kotu ta basu damar bibiyar bayanan da ke BVAS zai zama suna da ƙwararan hujjoji da za su yi amfani da su a nan gaba.
Ya kuma ce da zarar an goge komai to hakan na nufin matakin zai shafi hujjojinsu game da wannan shari’ar.
Shi kuwa lauyan INEC Tanimu Inuwa, ya buƙaci kotu ta hana damar, inda ya ce ba da umarni da Obi da jam’iyyarsa na iya shafar shirye-shiryen zaɓukan gwamnoni da ‘yan majalisun jihohi da ke tafe.
A gefe ɗaya kuma kotun sauraren ƙararrakin zaɓe da ke zamanta a Abuja, ta amince zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Najeriya Bola Tinubu ya duba kayan da INEC ta yi amfani da su yayin zaɓen shugaban ƙasa da aka yi ranar 25 ga watan Fabirairu.
A ranar Talata ne lauyan Tinubu, Akintola Makinde ya shigar da wata ƙara ta daban kan INEC da Peter Obi da LP da Atiku Abubakar da kuma PDP.
Tinubu ya ce idan aka amince masa duba kayan, hakan zai taimaka ma sa da jam’iyyarsa wajen “samun hujjojin da za su kare kansu da su a kotu” game da ƙalubalantar nasararsa da Obi da Atiku suke yi