INEC ta yi Watsi da Buƙatar ADC kan Cire Shugabanta

Hukumar zaɓen Najeriya ta yi watsi da kiraye-kirayen da wasu ke yi wa shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan ya sauka daga muƙaminsa.

Cikin wata sanarwa da INEC ɗin ta fitar ta bayayna kiraye-kirayen da hari kan dokokin da suka kafa hukumar.

A ranar Alhamis ne jam’iyyar ADC mai hamayya a ƙasar, ɓangaren David Mark ta buƙaci Mista Amupitan ya sauka daga muƙaminsa bayan da ta zarge shi da nuna ɓangaranci a aikinsa.

Matakin jam’iyyar na zuwa ne bayan da INEC ɗin ta sunayen shugabannin jam’iyyar ɓangaren David Mark, saboda umarnin kotu kamar yadda ta bayyana.

INEC ɗin ta ce kiraye-kirayen ba su da matsuguni, kasancewar doka ce ta naɗa shugaban nata.

“Dokar Najeriya ce ta samar da hukumar INEC. Kuma doka ce ta tanadfi naɗa shugabanninta kuma wa’adinsu,” in ji sanarwar.

“Shugaban INEC ba yana aiki ne ga kowace jam’iyya ko wata ƙungiya. Don haka duk wasu kiraye-kirayen cire shi daga wajen doka cin zarafi ne ga tsarin zaɓen ƙasa,” kamar yadda sanarwar ta yi ƙarin haske.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here