Dokar Zaman Gida: ‘Yan Kungiyar IPOB Sun Kona Fasinja a Jahar Imo
Mambobin IPOB sun yi wa wani fasinja kurmus a karamar hukumar Ahiazu Mbaise ta jahar Imo.
An gano cewa miyagun sun tare motocin dake zuwa Imo daga Umuahia kan dokar zaman gida da suka saka.
Kafin motar ta kai ga tsayawa, miyagun sun banka mata wuta, lamarin da yasa Nkwogu ya kasa fitowa har ya mutu.
Ahiazu Mbaise, Imo – Mambobin IPOB sun kone wani fasinja mai suna Nkwogu a karamar hukumar Ahiazu Mbaise dake jahar Imo sakamakon karya dokar zaman gida na dole da suka saka a ranar Litinin.
Tuni dai dukkannin harkokin kasuwanci suka tsaya a yawancin sassan jahohin kudu yayin da mazauna yankin suke bin dokar da aka saka, Daily Trust ta ruwaito.
An rufe makarantu yayin da aka hana dalibai masu rubuta jarabawar NECO fitowa domin rubuta jarabawarsu.
Miyagun sun bankawa motar wuta kafin ta tsaya
Read Also:
Daily Trust ta tattaro cewa mamacin yana cikin daya daga cikin motoci bas uku da miyagun suka tsare a titi.
Biyu daga cikin motocin kirar Hummer bas duk mallakin wani kamfanin sufuri ne mai suna Libra wanda suke tahowa daga Umuahia a jahar Abia lokacin da ‘yan ta’addan suka tsare matafiyan.
An tattaro cewa miyagun sun harba tayar, lamarin da yasa dole suka tsayar da motar.
Fasinjojin dake cikin bas din sun dinga gudun ceton rai inda aka harba daya daga cikin direbobin a kugunsa.
Fasinjan ya kasa fita saboda an bankawa bas din wuta kafin ta tsaya.
Ana musayar wuta tsakanin jami’an tsaro da miyagu
Daily Trust ta tattaro cewa an dinga jin harbe-harbe a wurin Banana Junction kan babbar hanyar Orlu zuwa Owerri yayin da ‘yan bindiga suka dinga artabu da jami’an tsaro.
Har a yayin rubuta wannan rahoton, mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jahar, CSP Mike Abattam bai dauka waya ba yayin da aka dinga kiransa.