Iran ta kai Sabbin Hare-Hare da Makamai Masu Linzami kan Isra’ila
Iran ta kai wasu sabbin hare hare da makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa kan Isra’ila da sansanonin sojojin Amurka da ke Kuwait da Jordan da Bahrain.
Jirage marasa matuƙa sun afkawa wani tankin mai a filin jirgin saman Kuwait, lamarin da ya haifar da tashin gobara.
Read Also:
A gefe guda kuma Isra’ila ta ce ta kai hari wasu wurare biyu da ake amfani da su wajen kera makamai masu linzami masu cin dogon zango a Tehran.
Hukumar sa ido kan ayyukan nukuliya ta Majalisar Dinkin Duniya IAEA, ta ce Iran ta sanar da cewa wani makami mai linzami ya kai hari kan wata tashar makamashin nukiliya a birnin Bushehr da ke kudancin kasar.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce hare-haren da Iran da Isra’ila ke kai wa a kusa da wuraren nukiliyar na da mummunan hatsari.






