Babu Hujja da ke Tabbatar da Cewa Iran na da Makami mai Linzami mai Dogon Zango da zai iya kai wa Turai – Birtaniya

 

Harba makamai masu linzami da Iran ta yi zuwa sansanin sojin haɗin gwiwa na Amurka da Birtaniya da ke tsibirin Indian Ocean na nuna yadda yaƙin na Gabas ta Tsakiya yake ta’azzara.

Duk da cewa hare-haren ba su riski asalin inda aka hara ba, rundunar tsaron Isra’ila IDF ta ce wannan ne karon farko tun farkon ɓarkewar yaƙin da aka yi amfani da makamai masu cin dogon zango mafi nisa, duk da cewa har yanzu Iran ba ta tabbatar da harba makaman ba.

Masana yanzu sun fara nazarin abin da harin ke nufi ne, ciki har da fargabar ko nan gaba za a iya kai hare-hare a manyan biranen Turai irin su Berlin da Paris da London?

Wani minista a Birtaniya ya bayyana cewa ”babu wata ƙwaƙƙwarar hujja da ke tabbatar da iƙirarin IDF cewa Iran na da makami mai linzami mai cin dogon zango da zai iya kai wa London”

“Makaman Iran masu linzami dama can an daɗe ana tattaunawa a kansu,” in ji Ghoncheh Habibiazad a tattaunawarsa da BBC.

“Duk da cewa Iran na nanata cewa tana ƙirƙirar makamai masu linzami ne domin kare kai, wasu na gani kai wa matakin makamai masu linzami masu cin dogon zango barazana ce ga tsaron yankin.”

Kimanin wata ɗaya baya ne aka shiga tattaunawa a game da nukiliyar Iran, inda ana tsaka da tunanin sake shirya wata tattaunawar ne kuma sai yaƙin Amurka da Isra’ila a Iran ya ɓarke.

Tsibirin Chagos – wanda a ciki ne akwai sansanin sojin haɗin gwiwa na Diego Garcia – yana da kimanin nisan kilomita 3,800 ne daga Iran.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here