Hukumomin Iran Sun Bayyana Cewa Sun Shawo Kan Gobarar da ta Tashi a Gidan Yarin Evin

 

Hukumomi a Iran sun bayyana cewa an shawo kan gobarar da ta tashi a gidan yarin ƙasar na Evin, sai dai har yanzu babu cikakkun bayanai.

Kafar yaɗa labaran ƙasar ta gwamnati ta ce an raunata aƙalla mutum takwas.

Wasu jerin bidiyoyi da aka wallafa a shafukan sada zumunta sun nuna yadda wutar ke ci gadangadan Htare da jin harbe-harbe da kuma ƙarar jiniya.

Gwamnan Tehran ya ce gobarar ta tashi ne sakamakon wata tarzoma da ta tashi tsakanin fursunoni.

Wakiliyar BBC ta ce gidan yarin na da muhimmanci matuƙa sakamakon a nan ne aka ajiye fursunonin siyasa na ƙasar da dama, da kuma wasu waɗanda aka kama bisa zanga-zangar da aka dinga gudanarwa kan mutuwar Mahsa Amini.

Tuni aka rufe hanyoyin da ke zuwa gidan yarin amma duk da haka akwai mutane da yawa da suka je wurin domin nuna goyon baya ga fursunonin.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here