Kasar Iran ta Shriya Taimakawa Najeriya Wajen Yaki da Ta’addanci
An yi bikin zagayowar shekara guda da kisan kwamamdan rundunar Quds na Iran, Qassem Soleimani.
Amurka ta dau alhakin kisan Qassem Soleimani yayin da ya isa kasar Iraqi.
Iran ta bayyana shirin taimakawa Najeriya wajen yaki da yan ta’adda.
Jakadan kasar Iran zuwa Najeriya, Ambasada Mohammad Alibak, ya bayyana cewa gwamnatin kasarsa shirye take da taimakawa Najeriya wajen kawo karshen ta’addanci.
Yayinda hirarsa da Nigeria Tribune, ranar Litinin, jami’in diflomasiyyan ya bayyana cewa kasarsa na damuwa kan irin halin tabarbarewan tsaron da ya addabi Najeriya.
Read Also:
Domin kawo karshen haka, ya bayyana cewa “Idan Najeriya ta shirya bamu hadin kai, zamu taimaka wajen kawo karshen ta’addanci a kasar.”
Yace: “Jamhurriyar Musulunci ta Iran ta samu kwarewa mai amfani a wannan fanni sakamakon dogon yakin da tayi da ta’addanci.”
“Tun daga farkon kungiyar ISIS da gwamnatin Amurka ta kirkira, marigayi Qassem Soleimani, na kan gaba wajen yaki da wannan kungiyar.”
“Ka’idar jamhurriyar Iran shine shirye take a koda yaushe domin hada karfi da kasashen da ke fama da matsalar rashin tsaro.”
“Sakamakon haka, mun gana sau tari da jami’an gwamnatin Najeriya kuma mun bayyana musu shirye muke da hada kai dasu kan lamuran tsaro.”
Alibak ya yi wannan jawaban ne ranar cika shekara daya da mutuwar tsohon kwamandan Sojin Iran, Qassem Soleimani.