Gwamnatin Iraq ta Gayyaci Manyan Jami’an Diflomasiyyar Iran da Amurka
Gwamnatin Iraq ta gayyaci manyan jami’an diflomasiyyar Iran da kuma Amurka bayan hare-haren da suka yi sanadin mutuwar mutane da kuma ƙara fargabar cewa ƙasar na iya shiga rikicin yaƙin Gabas ta Tsakiya.
Matakin na zuwa ne yayin da hare-hare kan ƙungiyoyin mayaƙa a cikin Iraƙi ke ƙaruwa, lamarin da ke tayar da hankali a tsakanin jami’an gwamnati da al’ummar ƙasar baki ɗaya.
Read Also:
Rahotanni sun ce gwamnatin Iraƙi ta kuma bai wa wasu daga cikin waɗannan ƙungiyoyi damar mayar da martani kan hare-haren da aka kai musu.
Wata ƙungiyar mayaƙa da ke da alaƙa da Iran ta zargi Amurka da kai wani hari da ya kashe wani kwamanda tare da raunata sama da mutum 12 daga cikin mambobinta.
A yankin Kurdistan kuma, wani hari da ake dangantawa da Iran ya yi sanadin mutuwar mambobi shida na wata ƙungiyar mayaƙan Kurdawa.
Haka zalika, ƙungiyoyin da ke da kusanci da Iran a cikin Iraƙi sun ci gaba da kai hare-hare kan sansanonin sojojin Amurka tun bayan fara wannan rikici.
Masu sa ido kan harkokin tsaro na ganin cewa irin wannan yanayi na iya ƙara jefa Iraƙi cikin wani sabon rikici, musamman idan ba a samu sassaucin rikicin da ke faruwa a yankin ba.















