Iyalan Marigayi MKO Abiola, Sun Nuna Rashin Jin Daɗin su Kan Yadda Gwamnati Tayi Watsi da Al’amuransu
A cewar iyalan marigayin wanda ya lashe zaɓen June 12, har yanzun gwamnati ta kasa cika alƙawurran da ta yi musu .
Kakakin iyalan, Rahaman Abiola, ya yaba wa shugaba Buhari bisa tabbatar da nasarar da kakansa ya samu a wancan Lokacin.
Mambobin iyalan marigayi MKO Abiola, sun nuna rashin jin daɗin su kan yadda gwamnati tayi watsi da al’amuransu.
Mai magana da yawun gidan, Rahaman Abiola, shine ya bayyana haka ranar Asabar 12 ga watan Yuni, a jahar Ogun, yace gwamnati ta kasa cika musu alƙawarin da tayi musu a shekarun baya, kamar yadda Punch ta ruwaito.
Da yake magana a Abekuta, babban Birnin jahar Ogun, Abiola yace har yanzun iyalan gidan su basu amfana da komai ba daga gwamnatin tarayya.
Read Also:
Sai dai duk da haka, wakilin iyalan marigayi Abiola, ya yaba wa shugaban Ƙasa Buhari bisa girmama tsohon ɗan siyasan da muƙamin zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Najeriya, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.
Yace:
“Munji daɗin matakin shugaba Buhari na giramama Abiola da GCFR kuma ya maida 12 ga Watan Yuni a matsayin ranar demokaraɗiyya a hukumance.”
“Jinjina ga Shugaba Buhari, amma har yanzun bamu amfana da komai ba daga FG.”
Hakanan kuma Rahaman Abiola ya yaba wa gwamnatin jahar Ogun kan yadda take murnar zagayowar wannan rana tare da iyalan gidan su.
Yace:
“A duk ranar 12 ga watan Yuni, gwamnatin jahar Ogun na iyakar bakin ƙoƙarin ta, mun jinjina musu akan haka.”
“Gwamna ya na zuwa har gida ya ƙara mana ƙarfin gwiwa, kuma ya tabbatar da mun yi murnar wannan rana a kowace shekara.”