Garkuwa da Kwamishina: Iyalan Kwamishinan Yada Labarai na Jahar Neja Sun Fara Tattaunawa da ‘Yan Bindigan

 

Gwamnatin jahar Neja ta sake jaddada matsayarta kan batun tattaunawa da ‘yan bindiga masu garkuwa da mutane.

Gwamnati ta ce tana kan bakanta, kuma ba za ta taba zama da ‘yan ta’adda masu cutar da al’umma ba.

Batun ya biyo bayan gano yadda iyalan wani kwamishina ke tattaunawa da ‘yan bindigan da suka sace kwamishinan.

Niger – Iyalan kwamishinan yada labarai na jahar Neja, Alhaji Mohammed Sani Idris, sun fara tattaunawa da wadanda suka sace kwamishinan, gwamnatin jahar ta ce.

Gwamnati ta kuma tabbatar da cewa wadanda suka sace kwamishinan sun tuntubi dangin inda a lokacin suka nemi N500m.

Sakataren Gwamnatin Jaha (SSG), Alhaji Ahmed Ibrahim Matane, ya fada wa THISDAY a wata hira ta wayar tarho jiya Laraba 11 ga watan Agusta cewa dangin ba za su iya biyan irin wadannan makudan kudaden da ake nema ba, “don haka suna tattaunawa da masu garkuwa da mutanen.”

SSG ya ce masu garkuwar ba su tuntubi gwamnatin jahar ba, inda ya nuna cewa “gwamnati ba ta tattaunawa da ‘yan bindiga ko masu garkuwa da mutane.”

Sai dai, a bangare guda SSG ya yi bayanin cewa gwamnati tana daukar matakai don tabbatar da cewa an ceto kwamishinan da aka sace, amma ya ki bayyana matakan da aka riga aka dauka saboda “dalilai na tsaro.”

Da aka tambaye shi ko gwamnatin jahar tana sane da inda ake tsare da Idris, ya ki cewa komai game da batun, saboda tsaro.

Wane hali kwamishinan ke ciki a yanzu?

Duk da haka, bincike mai zaman kansa ya nuna cewa masu garkuwa da mutanen sun kira iyalan kwamishinan a jiya Laraba inda aka tabbatar musu cewa yana cikin koshin lafiya.

An yi garkuwa da Idris ne daga gidansa da ke cikin garin Babantunga a karamar hukumar Tafa da misalin karfe 11 na dare a ranar Lahadin da ta gabata ne yayin da wasu mutane dauke da makamai suka afka masa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here