Jahilci da Duhun Kai Sune Manyan Matsalolin da ke Addabar Fulanin Rugga – Dakta Ahmad Gumi

Babban Malamin addinin Musulunci, Dakta Ahmad Gumi, ya ziyarci wasu rugage masu hatsari a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Sheikh Gumi ya gabatar da lakca ga al’ummar Fulani a rugage da ya ziyarta domin fadakar da su illolin da ke tattare da sace mutane.

A cewar Sheikh Gumi, jahilci da duhun kai sune manyan matsalolin da ke addabar Fulanin da ke zaune a rugage.

Sheikh Dakta Ahmad Gumi, fitaccen malamin addinin Islama, ya ziyarci wasu rugagen Fulani da suka yi kaurin suna wajen garkuwa da mutane a hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Daily Trust ta rawaito cewa rugagen da Babban Malamin ya ziyarta sun kasance tamkar tarko wurin matafiya a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Yayin da yake gabatar da jawabi a gaban dumbin al’ummar Fulani a garin Jere, Sheikh Gumi ya bayyana damuwarsa a kan yadda hanyar Kaduna zuwa Abuja ta zama abar tsoro saboda rashin tsaro.

Sheikh Gumi ya nuna takaicinsa akan yadda duhun jahilci ya lullube kwakwalwar Fulanin da suke garkuwa da mutane domin neman kudin fansa.

A cewarsa, bawa irin wadannan Fulani ilimin addini ko na zamani shine kadai mafita daga kangin jahilcin da ya jefasu cikin irin mummunar rayuwa.

Kazalika, ya dauki alkawarin cewa gidauniyarsa, duk da bata da karfi, zata gina makarantu guda biyu domin ilimintar da Fulani.

Ya kara da cewa za’a kara zabar wasu daga cikin Fulanin domin basu horon da ilimin da zasu ke koyar da sauran Fulani ‘yan uwansu.

Gumi ya bayyana cewa za’a kafa wani kwamiti da Fulani zasu ke shigar da korafinsu idan an yi musu wani rashin adalci domin nema musu hakkinsu.

A karshe, Sheikh Gumi ya rabawa al’ummar Fulanin wasu litattafai da zasu taimaka musu wajen sanin addini.

Daga cikin tawagar Sheik Gumi akwai Dakta Sulaiman Mahmud, babban limamin Masallacin Sultan Bello, jami’an tsaro, da wakilan kungiyoyin Malamai da dalibai.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here