Tsohon Jakadan Amurka, John Campbell ya yi Martani a Kan Lamarin Ministan Sadarwa
Wani tsohon jakadan Amurka a Najeriya, John Campbell ya yi martani a kan lamarin Pantami.
Campbell ya bayyana cewa Amurka ta fi damuwa da ayyukan ta’addanci ba tunani ba.
Tsohon wakilin ya kara da cewa ayyuka sun fi nauyi fiye da magana ko kalmomi kawai.
John Campbell, wani tsohon jakadan Amurka a Najeriya, ya ce ‘yancin fadin albarkacin baki da tunani na cikin tsarin Amurka.
Daily Nigerian ta ruwaito cewa Campbell ya ce gwamnatin Amurka ba za ta iya hana ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Isa Ali-Pantami bizarta ba, bisa lamari na zargi kawai.
Read Also:
Legit.ng ta tattaro cewa yayin da yake mayar da martani ga tattaunawar imel da jaridar The Punch a kan zargin a ranar Alhamis, 22 ga Afrilu, tsohon jakadan ya ce hudubar Pantami da sauran bayanan da ya yi a bainar jama’a ba za su iya zama mizanin sanya shi cikin jerin yan ta’adda ba.
Campbell, wanda ya yi aiki a matsayin jakada a Najeriya a tsakanin shekarar 2004 zuwa 2007, ya ce wani jami’in ofishin jakadancin zai so sanin lokacin da aka yi wa’azin Pantami da sauran bayanan da yayi a cikin jama’a.
Ya ce:
“Har ila yau, akwai tambaya game da ko yana bayar da fatawar tashin hankali ne, ko kuma afuwar da ya nema watsi ne da abunda ya fadi? Shin yanzu yana cikin ƙungiyar ta’addanci ta duniya? Ko kuma, wasu daga cikin ra’ayoyinsa sun yi daidai da na Osama Bin Laden? Kamar yadda kuka sani, ‘yancin faɗar albarkacin baki da tunani na tattare da tsarin Amurka.”