Jakadun Najeriya a Kasashen Ketare: Shugaba Buhari ya Aikawa Majalisar Dattawa Sunayen Tsofaffin Hafsoshin Tsaro

Muhammadu Buhari ya kara sunayen wadanda zai nada Jakadu a kasar waje.

Shugaban kasar ya aikawa Majalisa sunan tsofaffin hafsun sojojin da ya cire.

Hakan na zuwa mako guda bayan ya sauke shugabannin tsaro, ya nada wasu.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tura sunayen tsofaffin hafsoshin tsaro, inda ya bukaci a tantance su domin a ba su mukamai.

Mai ba shugaban kasa shawara a kan harkokin yada labarai ta kafafen zamani, Bashir Ahmaad, ya bada wannan sanarwa a shafinsa na Twitter.

Bashir Ahmaad ya bayyana cewa shugaban kasa ya aika takarda zuwa ga shugaban majalisa, Sanata Ahmad Ibrahim Lawan game da batun.

Mai girma Muhammadu Buhari ya na so tsofaffin shugabannin tsaro na kasar da ya sauke, su rike kujerar Jakadun Najeriya a kasashen ketare.

Shugaba Muhammadu Buhari ya dogara ne da sashe nan a 171 (1), (2) (c) da karamin sashe na (4) na kundin tsarin mulki wajen bada mukaman.

Kamar yadda hadimin shugaban kasar ya bayyana dazu nan, an aika sunayen mutane biyar ne zuwa ga majalisar dattawan a yau ranar Alhamis.

Ga sunayen kamar haka: Janar Abayomi G. Olonisakin (Rtd), Laftana Janar Tukur Y. Buratai (Rtd), da Vice Admiral Ibok-Ete Ibas (Rtd).

Haka zalika Air Marshal Sadique Abubakar (Rtd), da Air Vice Marshal Mohammed S. Usman (Rtd) sun shiga cikin wannan jeri da aka fitar.

Shugaban kasar ya nemi ‘yan majalisar dattawa su yi la’akari da bukatar da ya gabatar, su amince da nadin da ya ke neman yi na Jakadun Najeriya.

VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here