Jami’an Tsaro Sun Kama ‘Yan Ta’addan da Suka Kai Hari Cocin Owo
FCT Abuja – Hedkwatar Tsaro ta kasa ta ce ta kama yan ta’addan da suka kai hari a cocin St Francis Catholic Church a Owo, Jihar Ondo, rahoton The Nation.
Read Also:
Babban hafsan tsaro, Janar Lucky Irabor, wanda ya bada sanarwar yayin taro da shugabannin kafafen watsa labarai a hedkwatar tsaro a Abuja ya ce an kama bata garin ne tare da hadin kan hukumomin tsaro.
Yan ta’addan sun kai hari ne a cocin na Katolika a ranar Lahadi kuma suka bude wuta kan masu ibadan suka kashe fiye da mutane 30.
Lamarin ya faru ne a ranar 5 ga watan Yunin 2022.
Dakaci karin bayani …