Ayodele Fayose: Jami’an Tsaro Sun Dakile Harin da ‘Yan Bindiga Suka So yi a Taron PDP a Jahar Osun
Mutane sun shiga hargista a wurin taron jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) reshen yankin Kudu maso yamma da aka gudanar a Osogbo babban birnin jahar Osun a ranar Litinin, The Nation ta ruwaito.
Read Also:
Lamarin ya faru ne misalin karfe 6.45 na yamma a lokacin da wasu da ake zargin yan bindiga suka matsa kuda da kofar shiga wurin taron na WOCDIF event centre suka yi kokarin kutsawa.
Tsohon gwamnan jahar Ekiti, Ayodele Fayose yana daf da barin wurin taron ne sai yan daban suka yi yunkurin kustawa cikin wurin taron.
Jami’an tsaro sun dakile yunkurin kutsen da taimakon kwamishinan rundunar yan sandan jahar Osun, Olawole Olokode da wasu jami’an.
Jami’an tsaro sun ta yin harbe-harbe a sama domin fatattakar yan daban. Jami’an tsaro sun fice da Fayose cikin wata mota kirar Jeep mai bakaken gilashi ba tare da wani abu ya same shi ba.