Jam’iyyar PDP ta Kudu ta Fusata
NWC ta ruguza duk shugabannin Jam’iyyar PDP da ke jihar Ebonyi.
Shugabannin rikon kwarya na PDP a Kudu sun rasa mukamansu.
Jam’iyyar adawar ta yi wannan ne bayan Dave Umahi ya tafi APC Sauyin-shekar gwamna David Umahi ta fara tasiri a Ebonyi, inda yanzu har an fatattaki daukacin shugabannin jam’iyyar hamayyar da ke jihar.
Jaridar Vanguard ta fitar da rahoto cewa uwar-jam’iyyar PDP ta yi fatali da majalisar shugabannin jam’iyyar da ke aiki a kananan matakai na jihar.
Shugabannin PDP na mazabu, kananan hukumomi da kuma majalisar jiha sun rasa mukamansu.
Majalisar NWC da ke da alhakin gudanar da sha’anin jam’iyya ta bayyana haka a ranar Talata, 17 ga watan Nuwamba, ta bakin Kola Ologbondiyan.
Read Also:
Kola Ologbondiyan wanda shi ne sakataren yada labarai na jam’iyyar hamayyar, ya bada wannan sanarwa.
Mista Ologbondiyan ya ce NWC ta dauki wannan matsaya ne bayan wani zama na musamman da shugabannin jam’iyyar PDP su ka yi a ranar Talata.
Bayan haka, Ologbondiyan ya bayyana cewa NWC ta ruguza majalisar shugabannin rikon-kwarya na jam’iyyar da ke rike da shiyyar Kudu maso gabas.
Kamar yadda kakakin jam’iyyar hamayyar ya fada, dokar kasa da kundin PDP sun ba majalisar NWC ikon sauke duk wasu shugabanni idan ta kama.
Kawo yanzu, uwar-jam’iyyar ba ta bayyana wadanda za su rike guraben na rikon kwarya a jihar Ebonyi da yankin kasar kafin a gudanar da zabe ba.
A makon nan mun ji cewa tsohon gwamna jihar Imo, Sanata Rochas Okorocha, yana da burin zama shugaban kasar Najeriya a zabe mai zuwa na 2023.
Okorocha ya sanar da hakan ne bayan wasu taron magoya bayansa sun kai masa ziyara.