Abinda Jam’iyyar PDP Zatai Don Cin Nasara a 2023 – Atiku Abubakar
Atiku Abubakar ya yi jawabi wajen wani gangamin PDP a jihar Ebonyi.
Tsohon mataimakin shugaban Najeriyar ya yi kiran a samu hadin-kai.
Atiku ya caccaki masu sauyin-sheka daga PDP, su koma jam’iyyar APC.
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya ce sai jam’iyyar PDP ta hada kan gidanta kafin ta iya samun nasarori a zabukan 2023.
Jaridar Vanguard ta rahoto Alhaji Atiku Abubakar ya ce sai ‘Dan siyasa maras basira ne zai sauya-sheka daga PDP ya koma APC a marrar nan.
Wazirin Adamawa ya yi wannan bayani ne a wajen wani gangami da jagoran PDP, Dr. Onuoha Nnachi ya shirya a garin Afikpo, jihar Ebonyi.
Read Also:
“Idan mu na so mu samu nasara a zaben da za ayi nan gaba, dole PDP ta zauna lafiya, cikin hadin-kai a duka matakai, shi ne hanyar lashe zabe.”
Atiku Abubakar ya cigaba da cewa: “Mu na da kuri’u, da jama’a dabaru da shugabanni a Ebonyi.”
Ya ce: “Danyen aikin da gwamna ya yi abin takaici ne, dama siyasa ta gaji haka, don haka dole mu jajirce, PDP ta na da matukar karfi a jihar Ebonyi.”
Atiku ya ce nan gaba gwamnan Ebonyi David Umahi zai fadawa Duniya ainihin dalilin barinsa PDP. Oladimeji Fabiyi ne ya karanto jawabin na sa.
‘Yan siyasar da su ka halarci wannan taro sun hada da: Cif Ali Odefa, Sanata Michael Ama Nnachi, Hon. Iduma Igwariwey, da Hon. Fred Udeogu.
Gangamin ya kuma samu halartar irinsu Sylvester Ogbagba, Julius Ama Orji, Fidelis Nwankwo, Ajim Best, Emmanuel Kanodu, da kuma Abiam Onyike.