Yadda Jam’iyyar PDP ta Samu Rashin Jituwa a Wata Jaha

Abubuwa ya rincabe ta bangaren shugabancin PDP a jihar Ebonyi yayinda bangarori biyu ke yakin samun karfi.

Biyo bayan ficewar Gwamna Umahi daga jam’iyyar, an rushe shugabanninta na jihar sannan aka kafa kwamitin rikon kwarya.

Sai dai kuma, shugabannin jihar da aka tsige sun maka shugabancin jam’iyyar na kasa a kotu, wannan ya haifar da sabon rikici inda yan sanda suka shiga lamarin.

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Ebonyi ta fada cikin rikicin shugabanci dumu-dumu bayan sauya shekar Gwamna David Umahi zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Wani rahoto daga jaridar Daily Sun ya nuna cewa a ranar Lahadi, 20 ga watan Disamba, yan sanda sun karbe sakatariyar jam’iyyar na jihar ta arewa maso gabas.

A cewar jaridar, yan sandan sun dauki matakin ne biyo bayan wani kara da aka shigar kan shugabancin jam’iyyar a jihar.

Ku tuna cewa Legit.ng ta rahoto da fari cewa kwamitin masu ruwa da tsaki na PDP ta kasa ta rushe kwamitin shugabannin jam’iyyar na jihar bayan sauya shekar Gwamna Umahi. Sannan ta kafa na wucin gadi.

Sai dai, shugabannin da aka rushe, karkashin jagorancin ciyaman dinta, Onyekachi Nwebonyi, sun maka Shugaban jam’iyyar na kasa, Uche Secondus, PDP da zababben shugabannin a kotu.

Sannan Nwebonyi ya ci gaba da sanar da taro a sakatariyar wanda ya haddasa rudani a yayinda dayan bangaren jam’iyyar ya tunzura.

Yayinda lamarin ke a kudu har yanzu da yawan dage-dage, rundunar yan sanda a jihar sun je don kare sakatariyar.

A cewar hukumar tsaron, babu wanda za a bari ya shiga harabar har sai lokacin da kotu ta zartar da hukuncin sahihin Shugaban jam’iyyar a jihar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here