Jam’iyyu 17 na Kudancin Kasar Nan Sun Bayyana Ra’ayinsu Akan Atiku Abubakar a Zaben 2023

 

 

Wasu kungiyoyin siyasa a jahar Delta sun amince da tsayawar Atiku Abubakar a matsayin dan takarar shugaban kasa.

Wasu jam’iyyu 17 ne suka bayyana goyon bayansu ga tsayawar Atiku Abubakar a zaben 2023 mai zuwa.

Sun ce, Atiku ne ya fi cancanta ya tsaya takara a jam’iyyar PDP duba ga wasu halaye na kirki da yake dasu.

Delta – Shugabannin jam’iyyun siyasa 17 da kungiyoyin farar hula a jahar Delta a ranar Lahadin da ta gabata sun amince da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya tsaya takarar shugaban kasa a 2023.

Amincewar tana zuwa ne bayan bukatar gwamnoni jahohi 17 na kudancin kasar na neman shugaban kasa daga kudanci, Punch ta rawaito.

Gamayyar kungiyar Atiku Support Groups Initiative wacce ta sanar da amincewar ta yi ikirarin cewa bai kamata kabilanci ko bambancin siyasa su zama abin duba ga tsayar da dan takarar shugaban kasa a 2023 ba.

Babban Darakta na ‘CASGI ATIKU 2023, Mista Obinna Okorie, ya fadi haka a lokacin kaddamar da kungiyar a garin Asaba.

Okorie ya ce:

“Najeriya ta yau ta sha fama da matsanancin rashin tsaro, rashin aikin yi, kange matasa da kuma yawan karbar bashi ba tare da samar da wani abin kirki ba, wanda hakan ya jefa babbar kasar mu cikin hadari.

“CASGI ATIKU 2023 PROJECT kungiya ce ta Najeriya da ta ratsa kabila, kungiyoyin siyasa da sauran abubuwan da ke karkashin kasa.

“Jam’iyyar PDP za ta bai wa Mai girma Atiku Abubakar tikitin takarar shugaban kasa a shekarar 2023 saboda, Atiku Abubakar shi ne wanda ya fi dacewa ya ja ragamar mulkin PDP kan karagar mulki idan aka yi la’akari da ayyukansa na baya da kuma nuna karfin arzikinsa da gina tattalin arziki.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here