Hare-Haren Hamas: Jazaman ne sai an yi galaba a kan ‘yan ta’adda ko su wane ne – Theresa May
Tsohuwar Firaministan Birtaniya Theresa May ta bayyana hare-haren da Hamas ta kai a matsayin na kidahumanci.
Read Also:
“Jazaman ne sai an yi galaba a kan ‘yan ta’adda ko su wane ne, kuma a duk inda suke,” ta ce kuma ta yaba wa firaminista da sakataren harkokin wajen Birtaniya saboda matsayar da gwamnati ta dauka na goyon bayan al’ummar Yahudawa da kuma ‘yancin Isra’ila na kare kanta.
Ta nemi firaminista ya yi alkawarin ba zai yi kasa a gwiwa ba wajen hana rincabewar rikicin a yankin Gabas ta Tsakiya.