Jiga-Jigan APC da Suka Sauya Sheka Zuwa PDP a Jihar Kebbi

A halin da ake ciki a yanzu, jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na rasa karfinta a jihar Kebbi yayin da Peoples Democratic Party (PDP) ke kara karfi bayan wasu manyan jiga-jiganta guda takwas sun sauya sheka zuwa jam’iyyar adawar kasar.

Wani rahoton jaridar Punch ya bayyana cewa manyan jiga-jigan na APC a Kebbi sun sauya sheka ne bayan korafe-korafen cewa an yi kutse a tarukan jam’iyyar da aka gudanar a jihar.

Wadanda suka sauya shekar sune yan majalisa a majalisar dattawa, majalisar wakilai da majalisar dokokin jiha.

Masu sauya shekar sune:

Majalisar dattawa

1. Sanata Adamu Aliero (Kebbi ta tsakiya)

2. Sanata Yahaya Abdullahi (Kebbi ta arewa)

Majalisar wakilai

1.Honourable Mohammed Umar Jega (mai wakiltan mazabar Aliero/Jega/Gwandu a majalisar tarayya)

2. Honourable Abdullahi Zumbo (mai wakiltan Dandi/Arewa a majalisar tarayya)

Majalisar dokokin jiha

1. Habibu Labbo (mai wakiltan mazabar Gwandu)

2. Ismaila Biu (mai wakiltan mazabar Arewa)

3. Mohammed Aliero (mai wakiltan mazabar Aliero)

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here