Sanata da Jiga-Jigan APC Sun Sauya Sheka Zuwa NNPP a Jihar Bauchi
Jam’iyyar NNPP ta ribato Sanatan jihar Bauchi ta tsakiya a Majalisar Dattawa, Halliru Dauda Jika.
Sanata Halliru Dauda Jika ya fice daga APC bayan shan kashi a zaben zama ‘dan takarar Gwamna.
Arch. Audu Sule Katagum yana cikin jagororin da jam’iyyar APC ta rasa a jihar ana shirin zaben 2023.
Bauchi – Sanata mai wakiltar mazabar Bauchi ta tsakiya a majalisar dattawa, Halliru Dauda Jika ya fice daga jam’iyyar APC mai rinjaye a majalisa.
Solacebase ta kawo rahoto a ranar Lahadi, 19 ga watan Yuni 2022, Sanata Halliru Dauda Jika ya sauya-sheka ne zuwa jam’iyyar hamayya ta NNPP.
Sanatan ya shaidawa Duniya wannan mataki da ya dauka a wata wasika da ya aikawa shugaban APC na mazabar Kafin Madaki a garin Ganjuwa.
Wasikar ta shiga hannun jam’iyyar APC mai adawa a jihar Bauchi ne a ranar Alhamis da ta wuce.
Read Also:
Halliru Dauda Jika ya godewa shugabannin APC da suka ba shi dama ya nemi takarar kujerar gwamna a zaben fitar da gwanin da aka yi kwanaki.
Takarar Gwamna a APC
Jaridar The Gazette ta ce Sanata Jika ya shiga jam’iyyar NNPP ne bayan ya gagara zama ‘dan takarar gwamnan jihar Bauchi a APC a zabe mai zuwa.
Air Marshal Sadique Abubakar (mai ritaya) ya doke Sanata Jika a zaben tsaida ‘dan takarar gwamna. Abubakar ya samu kuri’a 370, Jika ya ci 278.
Wata majiya ta ce magoya bayan Sanatan mai shekara 46 suka dage a kan cewa ya koma NNPP bayan ya rubuta takardar da ta tabbatar da barinsa APC.
NNPP ta kara karfi a Bauchi
Jika shi ne Sanata na biyu da ya shiga jam’iyyar ta NNPP daga APC a ‘yan majalisar Bauchi. Kafin nan, Lawan Yahaya Gumau ya shiga jam’iyyar hamayyar.
Sauran ‘yan APC na jihar Bauchi da suka sauya-sheka sun hada da Audu Sule Katagum wanda ya rike mataimakin gwamna a jihar a gwamnatin da ya wuce.
Sauya-shekar ta na nufin NNPP ta samu karin magoya baya a kananan hukumomin Ganjuwa, Katagum da sauran inda ‘yan siyasar ke da magoya-baya.