Wasu Jiga-Jigan Jam’iyyar PDP Sun Koma Jam’iyyar APC a Nasarawa

 

Jam’iyyar APC mai mulki ta tarbi wasu manyan jiga-jigan PDP a jihar Nasarawa.

Masu sauya shekar sun rataya hukuncinsu na sauya sheka a kan ci gaban da aka samu a jihar karkashin Gwamna Sule.

Usman Labaran, daya daga cikin masu sauya shekar zuwa APC, ya bukaci mazauna jihar da su ba gwamnatin goyon baya.

Sansanin Peoples Democratic Party (PDP) na ci gaba da raguwa yayinda wasu jiga-jiganta suka sauya sheka zuwa All Progressives Congress (APC) mai mulki a jihar Nasarawa.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa wadanda suka sauya shekar sun hada da tsohon mamba mai wakiltan Toto/Gadabuke a majalisar jihar, Madaki Ada-Goje da kuma tsohon mai gudanarwar ci gaban yankin Gadabuke, Benjamin Musa Belodu da magoya bayansu.

Legit.ng ta tattaro cewa kakakin majalisar dokokin jihar Nasarawa, Ibrahim Balarabe Abdullahi, shine ya tarbi masu sauya shekar a yayin taron karshen shekara na masu ruwa da tsaki a APC wanda aka gudanar a karamar hukumar Toto.

Ya ce: “Kokarin gwamnatin APC wajen inganta tsaro a yankin, samar da hannun jari a fannin noma, ba yan asalin jihar mukaman siyasa da sauransu ne suka sanya su sauya sheka daga PDP zuwa APC.

“Ina ba magoya bayanmu da wadanda ke adawa tabbacin cewa gwamnati ta dauki alkawarin wanzar da ci gaba domin jam’iyyar ta ci gaba har bayan zaben 2023.”

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here