Jigon Jam’iyyar APC, Godwin Aigbogun ya Tsere Daga Hannun ‘Yan Bindiga

Shugaban jam’iyyar APC gunduma ta 9 a karamar hukumar Orhionmwon ta jihar Edo, Mista Godwin Aigbogun, ya kubuta daga maboyar wadanda suka sace shi.

Masu garkuwa da mutanen da ake zargin Fulani makiyaya ne, an ce sun bukaci iyalansa da su biya Naira miliyan 5, bayan da aka yi garkuwa da shi a hanyarsa ta komawa kauyensu daga gonarsa da ke Ologbo-nugu a yammacin ranar Litinin.

Sakataren Yada Labarai na Jihar Barista Peter Uwadiae, ya tabbatar wa da jaridar Punch cewa jigon ya tsere ne da safiyar Laraba kuma ya ce tuni ya koma ga iyalansa.

A cewarsa:

“Zan iya tabbatar muku da cewa ya kubuta daga hannun masu garkuwa da mutane. Ban san yadda ya yi ba amma dole ne in yaba masa da irin jarumtarsa. Ahalin jam’iyyar APC na jihar sun yi farin ciki da hakan. Yanzu yana tare da ahalinsa.”

Karin bayani na nan tafe…

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here