Dalilin da Yasa Jihata ke Zaune Lafiya – Gwamna Ganduje

 

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana dalilin da yasa suke zaune lafiya a jihar Kano, Arewa maso Yamma.

Ganduje ya ce jihar sa tsira daga rikicin addini da na kabilanci ne saboda yadda ake mutunta juna da hakuri tsakanin mazauna.

Sarkin Yarbawan Kano ya jinajinawa gwamnan sannan ya nemi a basu fili don su kafa sakatariyar kabilarsu a jihar.

Kano- Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje, ya danganta zaman lafiya da ake samu a jihar da mutuntawa da hakuri da ake yi tsakanin kabilu da addinai a jihar.

Ganduje ya kuma ce duk wasu kabilu da kungiyoyin addinai a kasar nan yan uwan juna ne, don haka akwai bukatar su rungumi zaman lafiya da hadin kai ba tare da la’akari da banbancinsu ba don samun ci gaba da zaman lafiya.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a karshen mako a Kano yayin da yake jawabi a fadar sarkin Yarbawa na jihar, Daily Trust ta rahoto

An dai gudanar da wani biki ne a fadar sarkin Yarbawar don murnar sarautar da aka baiwa gwamnan da matarsa a kwanakin baya a masarautar Ibadan.

A watan Yuni ne aka nadawa Ganduje da matarsa, Farfesa Hafsat Umar Ganduje sarautar Aare Fiwajoye da Yeye Aare Fiwajoye na kasar Ibadan.

Ganduje ya ce a shekarun baya, Kano ta yi fama da rikicin addinai da na kabilanci amma yanzu komai ya sauya saboda yadda ake nuna daidaito a tsakanin kabilu da addinai a jihar. Ya kara da cewa dukkanin kabilu da ke zaune a jihar ana daukarsu ne a matsayin yan asalin jihar.

Jaridar ta nakalto Ganduje yana cewa:

“Ko da ake fuskantar matsalolin tsaro, muna tabbatar da ganin cewa mun ba cocinanmu kariya kamar yadda muke ba masallatanmu, saboda dukkanmu mutane ne kuma Allah ya yi mu daban-daban. Don haka ya zama dole mu gode ma Allah a kan haka, sannan mu rungumi junanmu don rayuwa a matsayin yan uwan juna.”

Sarkin Yarbawan Kano, Murtala Al’imash Otisese, ya ce bikin ya zama dole saboda sarautar ta dace da gwamnan da matarsa kuma ya cancanci karramawa.

Ya kuma bukaci gwamnan da bayar da fili don gina sakatariyar Yarbawa a jihar, wanda gwamnan ya yi alkawarin aikata hakan.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here