Jirgin ƙasa a Jahar Legas ya yi ciki da Motar Bus Dauke da Fasinjoji
Lagos- Wasu Fasinjoji sun jikkata wasu kuma suka tsallake rijiya da baya bayan wani Jirgin ƙasa ya yi ciki da wata Motar Bus ta haya a jihar Legas, kamar yadda Tribune Online ta rahoto.
Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne bayan Direban Motar ya yi kunnen uwar shegu da gargaɗin mutane na ya jinkirta Jirgin da ya kusanto ya wuce.
Lamarin ya faru ranar Talata a kan layin dogo da ya ratsa ta hanyar Ilupeju bye-pass lokacin da Direban Bus Toyota Hiace ya ƙi dakata wa bayan jami’an ba da hannu sun umarci Motoci su tsaya jirgi ya wuce.
A cewar jami’an ba da agajin gaggawa LASEMA ta jihar Legas, waɗan da suka yi saurin zuwa wurin bayan samun rahoto, bisa tilas Fasinjojin suka fice daga Motar.
Read Also:
A cewar hukumar LASEMA, duk da haka mutum biyu sun jikkata yayin kokarin tsira da rayuwarsu, an ba su taimakon gaggawa daga bisani aka kai su babban Asibitin yankin.
LASEMA ta ce:
“Ɗaukin da jami’an mu suka kai cikin lokaci ne ya daƙile munin lamarin wanda ka iya sanadin rasa rayuka a Ilupeju bye-pass ranar 10 ga Watan Mayu, 2022.”
“Lokacin da jami’ai suka isa sun gano wata Motar Bas mai lamabar rijista EKY 888 XW da Jirgin kasa ne suka haɗe. Rashin kulawa da gangancin direban Bas ne ya jawo hatsarin.”
“Bayanan da muka samu sun nuna cewa an dakatar da Direban lokacin da zai ratsa amma ya yi kunnen uwar shegu da umarnin jami’an ba da hannu da ke aiki a wurin.”
Shin akwai wanda ya rasa rayuwarsa?
Hukumar LASEMA ta ƙara da cewa bisa sa’a babu wanda ya rasa rayuwarsa sanadiyyar hatsarin, sai mutum biyu da suka ji raunuka kuma ana kula da lafiyarsu.