Jirgin ƙasa ya Take Ma’aikata 5 a Italiya

 

Ma’aikatan layin dogo biyar sun mutu, bayan wani jirgin kasa mai karfin gaske ya banke su a kasar Italiya.

Ma’aikatan dai na ɗauke ne da kayan aikin da za su yi amfani da su wajen gyaran wani layin dogo a lokacin da jirgin ya banke su, a kusa tashar jirgi da ke Turin.

Rahotanni sun bayyana cewa wasu ma’aikatan biyu da ke tare da 5 din da iftila’in ya ritsa da su, sun tsallake rijiya da baya.

A ɓangare guda kuma ‘yan sanda sun ce suna gudanar da bincike a kan lamarin.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com