IBB ne ya sa Goodluck Jonathan ya Dare Kan Kujerar Shugaban Kasa a 2010 – Femi Otedola

 

Femi Otedola ya bada labarin yadda ya yi da Ibrahim Badamasi Babangida a 2010.

Attajirin yace IBB ne ya sa Goodluck Jonathan ya dare kan kujerar shugaban kasa.

Hakan ya faru ne lokacin da Ummaru ‘Yar’adu ya bar Najeriya babu wani shugaba.

Abuja – Kasurgumin ‘dan kasuwan nan, Femi Otedola, yace Ibrahim Badamasi Babangida ya sa Dr. Goodluck Jonathan ya hau kujerar shugaban Najeriya.

Premium Times ta rahoto Femi Otedola yana cewa tsohon shugaban kasar ne ya ba Goodluck Jonathan shawarar ya zauna a kujerar Ummaru ‘Yar’adua.

Ummaru ‘Yar’adua ya bar Najeriya babu shugaban rikon kwarya

Otedola ya yabi yadda tsohon shugaban kasan na soja ya bi, ya shawo kan matsalar da Najeriya ta shiga a lokacin da Marigayi ‘Yar’adua yake jinya a ketare.

A littafinsa mai suna “business lessons” (darusan kasuwanci), da zai fito a watan Nuwamban bana, Otedola ya ce shi ne ya zama ‘dan-aiken Babangida.

“A lokacin da Yar’Adua bai mika mulki ga mataimakinsa ba, ya tafi kasar waje neman magani, an shiga wani hali saboda an bar kasa babu shugaba.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here