Sheikh Kabara ya yi kira ga Babban Alƙalin Najeriya da ya Shiga Shari’arsa

 

Sheikh Abduljabbar Kabara ya yi kira ga babban alƙalin Najeriya da ya shiga lamarin shari’ar da yake da gwamnatin Kano.

Malamin addinin musuluncin ya bayyana haka ne a wata wasiƙar ƙorafi da ya rubuta zuwa ga babban alƙalin, inda ya yi zargin ana jan ƙafa da gangan bayan ɗaukaka ƙara da ya yi kan hukuncin kisa da aka yanke masa bisa zarginsa da ɓatanci ga Annabi Muhammadu.

A wasiƙar, ya yi ƙorafe-ƙorafe da suka haɗa da jan ƙafa da gangan hana shi samun cikakken bayanan shari’ar da zargin rashin daidaito da nuna son kai.

Haka kuma ya yi zargin ba a yi masa adalci a shari’ar, sannan ya dasa alamar tambaya da shakku kan ikon da kotun shari’ar ke da shi na sauraron ƙarar tun a farko.

A watan Disamban 2022 ne kotun shari’ar musulunci a Kano ta yanke wa malamin hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan samunsa da laifin ɓatanci ga Annabi a cikin wa’azinsa.

Bayan hukuncin ne malamin ya ɗaukaka ƙara, inda ya bayyana cewa ba a masa adalci a ƙaramar kotun ba, sannan ya ce ba a ba shi damar bayyana nasa ɓangaren ba, inda ya ƙara da cewa kalaman da ake magana daga littafai ya karanta su, kuma bai karanta da nufin cin mutunci ko ɓatanci ga Annabi ba.

Ya ƙara da cewa bai aikata laifi ba, sannan ya ce idan har za a saurara shari’ar da adalci, yana da yaƙinin za a fahimce shi, kuma a wanke shi.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here