Abduljabbar Kabbara ya Nemi Shugaban Alkalai na Jihar Kano da ya Sauya Masa Kotu
Malam Abduljabbar ya nemi Shugaban Alkalai na Jihar Kano, Dokta Tijjani Yusuf Yakasai ya sauya masa kotun da ke sauraren shari’arsa.
Abduljabar Nasiru ya zargi Alkali Ibrahim Sarki Yola, da hana shi damar kare kansa yadda ya kamata.
Abduljabar yace bai gamsu da yadda shari’ar sa ke tafiya da kuma mu’amalar da alkali ke yi da bangarorin da suka shigar da karar sa.
Jihar Kano – Babban malamin da ake zargi da yiwa Annabi batanci, Abduljabbar Nasiru kabara ya nemi a canza masa kotun dake sauraren karar sa kamar yadda Aminiya ta rawaito.
Read Also:
Abduljabar ya nemi Shugaban Alkalan jihar Kano, Dokta Tijjani Yusuf Yakasai ya sauya masa kotun ne saboda zargin rashin ba shi damar kare kansa yadda ya kamata da Mai Shari’a Ibrahim Sarki Yola ke yi.
Abduljabbar Nasiru Kabbara wanda jigo ne a Darikar Kadiriya ya bayyana hakan ne a zaman kotun da aka yi a yau ranar Alhamis 21 ga watan Yuli, 2022.
Shehin Malamin ya gabatar da bukatan sa ne bayan da kotun ta nemi sanin dalilin da ya hana lauyansa halartar zaman kotun.
Da yake bayani, Abduljabbar ya shaida wa kotun cewa ya rubuta wa Shugaban Alkalan Jihar takardar neman a sauya masa kotu saboda rashin gamsuwarsa da yadda shari’ar ke tafiya da yadda alkalin kotun ke mu’amala da bangarorin suka shigar da karar sa.
Karin bayani na tafe.