Babban Bankin Najeriya ya Kaddamar da Tsarin Gwajin Kudin Intanet
Babban bankin Najeriya ya sanar da ranar da zai fara gwajin kudaden intanet da ya kirkira.
A baya babban bankin Najeriya ya haramta amfani da kudaden intanet, amma yanzu ya yi nashi da tsari.
Babban bankin ya bayyana yadda yake aikin kirkirar fasahar tun shekarar 2017 a can baya.
Babban Bankin Najeriya ya ce zai kaddamar da tsarin gwajin kudinsa na intanet a ranar 1 ga Oktoba, 2021.
Read Also:
A cewar Nairametrics, CBN tare da masu ruwa da tsaki sun bayyana kudirin su na kudin intanet a wata ganar yanar gizo mai zaman kanta wacce aka gudanar a ranar Alhamis, 22 ga watan Yulin 2021.
A wani rahoto da jaridar Punch ta fitar kwanan nan, Gwamnan Babban Bankin na CBN, Godwin Emefiele ya sanar da cewa bankin na aikin samar da kudin na intanet a yayin taron Kwamitin Banki na 306.
Nairametrics ta ce, majiyarta mai zaman kanta ta ce za a kaddamar da shirin ne a ranar 1 ga Oktoba, 2021.
Ta ce a jawabin da Daraktan sahen IT, Rakiya Mohammed ta yi a karshen taron ta bayyana cewa Bankin ya kasance yana gudanar da bincike a game da kudaden intanet na babban bankin tun shekarar 2017 kuma hakon kan iya cimma ruwa kafin karshen wannan shekarar.
Ana lakafta sunan aikin da Project GIANT kuma zai yi amfani da tsarin Blockchain na Hyperledger Fabric.