Gwamnatin Kaduna Za ta Dauki Sabbin Malamai 10,000

 

Yayin da aka kori wasu malamai da dama bisa zargin rashin cancanta, gwamnatin Kaduna za ta dauki sabbin malamai.

Bayanai sun bayyana yadda gwamnati ta tsara kafar yanar gizo domin fara daukar ma’aikata a ma’aikatar ilimi ta jihar.

A baya gwamna El-Rufai ya sanar da daura aniyar daukar malamai 10,000 domin kawo gyara a fannin ilimi na jiharsa.

Jihar Kaduna – Gwamna Nasir El-Rufai ya amince da tsarin aiki na hukumar kula da ilimin bai daya ta jihar Kaduna (KADSUBEB) na daukar malamai 10,000 ta kafar yanar gizo.

Wata sanarwa da Shugaban Hukumar KADSUBEB, Malam Tijjani Abdullahi ya fitar, ta bayyana cewa hukumar ta baiwa Jami’ar Jihar Kaduna (KASU) aikin kirkira kafar daukar ma’aikata, wadda za ta fara aiki a ranar Alhamis, 21 ga Yuli, 2022.

Hakazalika, sanarwar ta ce masu bukatar cike fom din neman aikin dole ne su zama masu NCE da masu digiri na farko a fannin Ilimi (B.Ed, B.A EED, B.Sc, Bd, B.Tech daga jami’o’in da gwamnati ta amince dasu.

Yadda tsarin zai kasance

Hakazalika, rahoton ya ce, za a bude kafar na tsawon makonni biyu daga ranar ranar 21 ga Yuli, 2022, zuwa 5 ga Agusta, 2022.

A bangare guda, bayan kammala cike fom din, sanarwar ta ce za a gudanar da kwarya-kwaryar jarrabawar tantancewa ta yanar gizo a garuruwa uku na jihar da suka hada da Kaduna, Zaria da Kafanchan.

Da yake magana kan yadda za a bi wajen tantance nasarar wadanda suke neman aikin, ya ce:

“Wadanda suka samu 75% a jarrabawar, wanda shi ne ma’aunin da gwamnatin jihar Kaduna ta tsara, za a gayyace su ne domin tattaunawar baki da baki.”

Malam Tijjani ya kuma ce ana sa ran wadanda suka yi nasara za su zo da asali da kwafin takardunsu a wurin tattaunawar.Za a duba ainihin takardun yayin da za a ba da kwafinsu ga kwamitin tantancewa.

Shugaban hukumar ya yi alkawarin cewa hukumar ta KADSUBEB za ta aike da dukkan kwafin takardun nan take zuwa makarantu daban-daban domin tantancewa.

A cewarsa, wadanda suka yi nasara za a dauka aiki sannan kuma KADSUBEB za ta buga sunaye da bayanan wadanda aka dauka aiki.

Hakazalika, hukumar ta ce za ta tabbatar da tura malaman bangarori daban-daban na jihar, ciki har da kauyuka da karkara.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here