Ka fi Masu Zaginka Gaskiya Dattijo – Masoyin Buhari

 

Fitaccen masoyin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Sirajo Saidu Sokoto, ya sake jaddada kaunarsa ga shugaban kasan.

A wallafar da yayi a Facebook, ya sanar da cewa dattijon shugaban kasan yafi masu zaginsa gaskiya kuma mutuwa ce kadai ce zata raba su.

Sanannen masoyin shugaban kasan ya saba caccakar masu sukar Buhari duk da sace ‘yan uwansa maza 5 da ‘yan bindiga suka yi a Sokoto shekarar da ta gabata.

Wani ‘dan gani-kashenin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tabbatar da cewa mutuwa ce kadai za ta raba shi da shugaban kasan.

Idan za mu tuna, Sirajo Saidu Sokoto a shekaar da ta gabata ta yi bore tare da sanar da cewa baya tare da shugaban kasan bayan ‘yan bindiga sun yi awon gaba da ‘yan uwansa maza har biyar a jihar Sokoto.

Saidu fitaccen masoyin shugaban kasa Muhammadu Buhari ne a kafara sada zumuntar zamani ta Facebook kuma an san ya kware wurin caccakar masu zukar shugaba Buhari da jam’iyyar APC.

A ranar Juma’a, 29 ga watan Yulin 2022, ya sake jaddada goyon bayansa da kauna ga shugaban kasan Muhammadu Buhari.

“Ka fi masu zaginka gaskiya dattijo. Mun yi alkawarin mutuwa ce kadai zata raba mu da Buhari,” ya rubuta.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here